Amurka Na Zargin Pantami Da Goyon Bayan Ta'addanci


Daga Muhammad Farouk

Hukumomin tsaron sirri na kasar Amurka ta sanya Ali Isa Pantami cikin jerin wadanda take sanyawa ido da suke goyon bayan ta'addanci a duniya, Jaridar MADOGARA ta labarto. 

Alhaji Isa Pantami a yanzu shi ne Ministan sadarwa da tattalin arzikin fasaha na Nijeriya, kuma shi ne mataimakin Sakataren Majalisar shari'a ta koli ta Nijeriya. Sannan tsohon dalibi ne da yake bin manhajin Salafiyya. Ya yi karatunsa a kasar Saudiyya da kuma gabas ta tsakiya da sauran wadanda Amurka take zargi da ta'addanci. 

Kafin nada shi a matsayin Ministan sadarwa da tattalin arzikin fasaha ta Nijeriya, Pantami ya kasance fitaccen Malamin addinin Musulunci da Amurkan ta yi zargin; "yana yada tsattsauran ra'ayi akan kasar Amurka. Tare da goyon bayan kungiyar ta'addanci ta AlQaeda", inji su. 

Amurkan ta ce ministan har wala yau makusanci ne ga tsohon shugaban Boko Haram, Marigayi Muhammad Yusuf, wanda ta ce suna da ra'ayi guda a kan jihadi. 

A cewar rahoton na hukumomin sirri na tsaron Amurka, sun bayyana cewa ministan har wala yau yana da alaka ta kut da kut da Abu Quatada al Falasimi da kuma sauran jagororin AlQaeda, wanda Amurkan ta ce ministan ya yi jawaban goyon baya ga jagororin AlQaeda din a jawabansa daban-daban da aka wallafa a YouTube. 
 
Rahoton ya ce a daya daga cikin jawaban Pantami ya yi jinjina ga Abu Musab Al-Zarqawi, daya daga cikin manyan jagororin AlQaeda da ya shiga kungiyar bayan ya koma Afghanistan a karshen harin ta'addanci da aka kai na 11 ga watan Satumba a babbar kasuwar duniya ta Amurka.  

 Rahoton ya nakalto zancen Pantami da ya yi akan Abu Musab, inda Pantami ya bayyana cewa; "a karkashin jagorancin Osama, ya kasance Kwamandan sojin yanki na AlQaeda bisa goyon bayan Maula Umar (shugaban Taliban). Bayan harin 11 ga Satumba, ya samu mummunan rauni a kafarsa wanda ya yi jinyarsa a Iraqi, inda ya kwashe dogon lokaci kafin ya warke", inji Pantami. 

Pantami ya ci gaba da cewa; “bayan makiya Allah sun kai wa Iraqi hari, wannan babban mujahidi ya jagoranci kungiyar domin yaki da Amurka da masu goya musu baya a Iraqi", ya lurantar.

Jaridar SUNDAY INDEPENDENT da ake bugawa a Nijeriya ta wallafa labarin; 

Post a Comment

0 Comments