An Fitar Da Sunayen Dalibai Na Jami’ar Greenfield Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

 Wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari Jami’ar Greenfield dake jihar Kaduna a daren ranar Talata, inda suka kashe mutum daya da awon gaba da dalibai da dama. 

Ita dai Jami’ar Greenfield jami’a ce mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba, wacce ta fara aiki shekaru uku da suka gabata, kuma mazauninta na kan titin Kaduna zuwa Abuja. 

Majiyarmu ta Jarirdar DESERT HERALD ta labarto cewa; wanda ya assasa jami’ar ya tabbatar musu cewa; tabbas an kai hari Jami’ar, kuma ‘yan bindiga sun sace dalibai da dama. Wanda ya ce ya zuwa yanzu ba su tabbatar da adadin daliban da aka sace ba. Amma majiyar tamu ta ce ‘yan bindigar sun kashe ma’aikacin Jami’ar daya a yayin da suka kai harin.  

Majiyarmu Ta Zayyano Sunyen Dalibai maza da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su: 

1. Abraham Akinje

2. Fortune Alhassan

3. Miracle John

4. Miracle Turman

5. Jesse Jakiri

6. Joseph Davies

7. Abdullahi Yusuf

8. John Yari

9. Micheal Samson Ladan

10. Abdulkareem Ibrahim

11. Kabir Hamisu

12. Lemuel Adamu

13. Isreal Antonio

14. Isreal Musa

15. Nelson David

16. Mariam Nalado

17. Abdulkadir Abubakar


Post a Comment

0 Comments