An Gudanar Da Zazzafar Zanga-zangar Goyon Bayan Buhari A Ingila

Daga Muhammad Farouk

Magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari a Ingila sun gudanar da zanga-zangar martani da nuna goyo baya ga shugaban kasar a daidai lokacin da ake duba lafiyarsa a kasar ta Ingila. 

Sun gudanar da zanga-zangar ne a kofar gidan shugaban kasar da ake kira da Nigerian House da ke Ingila.

Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu shi ne ya wallafa hotunan zanga-zangar a shafinsa na sada zumunta na Facebook. 

Garba Shehu ya wallafa cewa: "hotunan wadansu masu kishin kasa sun taru a kofar gidan Nijeriya dake Ingila domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. 


Sun yi zanga-zangar ne a wani mataki na mayar da martani ga wadanda suka kwashe kwanaki suna zanga-zangar neman wulakanta shugaban kasar a Ingila wanda suka faro shi a shafukan sada zumunta da taken #HarassBuhariOutOfLondon

Inda suka kwashe kwanaki suna gudanar da zanga-zangar. 

Post a Comment

0 Comments