An Kai Wa Tashar Nukiliyar Iran Hari Ta Intanet


Iran ta sanar da cewar an yi wa cibiyar ta ta Nukiliya ta Nantanz kutse ta Intanet a wannan Lahadin kuma ta ce za ta dau dukannin matakan da suka kamata wajen ganin mayar da martani ga wadanda suka yi kutsen.

Shugaban shirin Nukiliya na kasar ta Iran Ali Akbar Salehi ne ya sanar da hakan ta kafar talabijin mallakin gwamnatin kasar, inda ya ce harin ya shafi bangaren rarraba wuta na cibiyar, amma dai bai haifar da wata gagarumar matsala ba sai dai ya ce Tehran ba za ta daga kafa ga wadanda suka yi kutsen ba.

Wannan harin da aka kai dai na zuwa ne kwana guda bayan da Iran din ta sanar da yin gwaji na wata sabuwar nau'ra ta inganta sinadarin Uranium da ke aiki cikin gaggawa fiye da wadda take da shi a halin yanzu.

Iran dai na shan suka daga kasashen duniya da dama kan shirin na ta na Nukiliya wanda ake zargin tana yinsa ne domin samar da makamin kare dangi, sai dai ta sha musanta zargin hakan kamar yadda rahoton DW Hausa ya fayyace.

Post a Comment

0 Comments