An Sanar Da Ranar Jana'izar Shugaba Idris Deby


BBC Hausa ta labarto cewa; an sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar da za a yi wa Shugaba Idris Deby Itno jana’izar ban girma, wanda ya rasu yayin fafatawa da ‘yan tawaye da ke arewacin kasar.

Za a fara da macin soji, daga nan dan marigayin, kuma wanda sojoji suka sanar zai mulki kasar wato Janar Mahamat Kaka zai gabatar da jawabi.

Sanarwar ta ce an gayyaci shugabannin wasu kasashe wajen jana’izar.

Takardar yadda jana’izar za ta gudana dai an yada ta tare da sa hannun fadar shugaban kasa.
Post a Comment

0 Comments