Daga Auwal Adam
Gwamntin
Ribas a karkashin gwamna Nyesom Wike ta ayyana dokar hana zirga-zirga a cikin
dare a jihar tare da cewa babu shiga kuma babu fita.
Cikin
jawabin da ya yi wa al’ummar jihar, gwamna Nyesom Wike ya ce dokar za ta fara
aiki da daren yau Laraba.
Sanya
dokar ya biyo bayan sabbin hare-hare da wasu ‘yan bindiga da ba a gano su ba
suke kai wa kan jami’an tsaro.
“Gwamnatin jihar Ribas ta yanke shawarar
takaita shige da fice a jihar kan iyakokin jihar na tudu,” a cewar Wike.
Dokar
wadda za ta fara aiki daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe, ta shafi mutane da
ababen hawa.
Majiyarmu
ta labarto cewa; gwamnan ya bayyana cewa an girke jami’an tsaro domin tabbatar
da jama’a sun bi dokar.
0 Comments