Ana Yunkurin Sakin Kirkirarren Bidiyon Karya Domin A Bata Min Suna, Inji Pantami

 

Daga Muhammad Farouk

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya yi zargin cewa ana yunkurin sakin wani bidiyo da aka kirkira domin a bata masa suna.

Ministan sadarwar ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakinsa, Uwa Suleiman, inda ya ce ba zai yadda mutuncinsa da ya dade yana ginawa a bata masa ba.

 “mun samu bayanan sirri masu karfi da ke nuni da cewa wadansu kusoshi da suke kashe makudan kudade wajen daukar nauyin kamfen din bata sunan ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, sun shirya tsaf domin daukar mataki na gaba akan shirin na su”, inji Uwa Suleiman.

Ministan ya ci gaba da cewa; “a wannan lokacin, wadannan kusoshin marasa mutunci sun hada hannu da wadanda suke hulda da su kamar yadda suka ba, inda za su saki wani bidiyo da suka kirkira da zai nuna ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali a wani irin yanayi da zai bata masa suna”, inji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; “mun yi mamaki bisa wannan yunkurin na su wanda yake nuna yadda suka zaku duk da nakasu da faduwa da suka rika samu akan ministan a yunkurinsu na baya”, ta lurantar.

 “bayan sun kirkiri karya da gaskiya suna alakanta ministan da ta’addanci, duk da hujjojinsa na yakar kungiyar ta’addanci na Boko Haram, wadannan mamuguntan ba su tsaya nan ba, sun tashi haikan wajen kirkirar takardar boge da ka iya haifar da tashin hankali a kasarnan. Wanda shima cikin ikon Allah da taimakon ‘yan Nijeriya masu son zaman lafiya, shima shirin na su ya fadi warwas”, ta tabbatar.

Uwa Suleiman ta karkare da cewa; “wannan sanarwar domin shelantawa al’umma shirin su da suke kokarin yi ne tare da gargadin wadanda suke hakan akan abin da ka iya biyo baya idan suka aikata hakan. Mai girma ministan ba zai zauna haka nan ya rika ganin mutuncinsa da ya dade yana ginawa a matsayinsa na shugaban al’umma, Malamin addinin musulunci, kuma ma’aikacin gwamnati wadansu da ake biya na bata shi da yi masa cin kasa ba tare da gaskiya ko tsoron Allah ba”, ta tabbatar. 

Post a Comment

0 Comments