APC Na Neman Mutum Mai Ilimi Da Zai Gaji Shugaba Buhari A 2023

 

Daga Muhammad Farouk 

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, na neman mutum dan Nijeriya mai ilimi da za su tsayar takara a zaben shekarar 2023.

Jam’iyyar APC domin kaucewa zarginta da tsayar da dan takarar da ba shi da takardun makaranta kamar yadda aka zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani kotu ta wanke shi, ta nemi da dukkanin membobinta da su kasance cikin shiri domin fuskantar zaben da za a yi.

 “muna neman mutane masu ilimi da za su tsaya takara a kowanne mukami a Nijeriya. A wannan lokaci, idan ba ka yi nasara ba, za a biya ka asarar da ka yi”, inji APC.

“dole ne a tsaya takara, mata ma za su tsaya takara, gajiyayu ma za su tsaya takara. Haka zalika ma matasa masu kwazo za su tsaya takara”, suka jaddada.

 “ku sani, shugaban jam’iyyar mutum ne mai sauraron kowa, duk abin da kuke da bukata domin ku kai ga nasara, zamu yi muku”, inji John Akpanudoedehe, Sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APC din a ranar Talata a Abuja.

John Akpanudoedehe ya bayyana hakan ne a wani taro da APC din ta shiryawa ‘APC Professionals’ Forum’ a Sakatariyar jam’iyyar domin bayyana nasarori da ci gaban da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo.

Akpanudoedehe, ya wakilci gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC ne a taron, inda ya jinjinawa dandalin bisa wayar da kan ‘yan Nijeriya akan nasarorin da gwamnatin ta kawo.

 


Post a Comment

0 Comments