Ba Gaskiya Bane Cewa Amurka Ta Ce Pantami Na Goyon Bayan Ta'addanci -BincikeRahoton Jaridar Aminiya 

Rahoton da ke yawo a wasu kafafen yada labarai na intanet a Najeriya cewa gwamnaitn Amurka tana zargin Dr Isa Ali Pantami da alaka da ta'addanci babu gaskiya a cikinsa.

Labarin zargin sanya sunan Ministan Sadarwan a cikin jerin mutunen da Amurka take nema bisa zargin daukar nauyin ta'addanci, ya tayar da kura matuka. 

Daga bisani kafar NewswireNGR da ta ruwaito labarin daga Daily Independent ta janye shi tare da cewa, "Muna neman afuwar masu karatu saboda labarin da muka wallafa, muna kuma neman yafiyar Ministar Sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Pantami."


Ta bayyana cewa bayan nakalto labarin daga Daily Independent, "Mun gudanar da bincike mai zaman kansa a kan labarin [namu] kuma mun gano cewa ba daga hukumar Amurkan da aka ruwaito ta fito ba."
 
Janye labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin Ministan, Uwa Sulaiman ta fitar da sanarwa cewa labarin ba shi da makama, sannan hankali ba zai dauka ba a ce duk da irin ayyukan da Pantami yake yi na yaki da ta'addanci, a same shi da hannu a abin da ake zargin.

"Tsare-tsaren farko da Pantami ya kawo a matsayinsa na Minista sun hada da yin rajistar layukan waya da nufin dakile ayyukan ta'addanci, wanda ya taka burki ga yadda a baya ake sayarwa da kuma yin rajistar layukan waya barkatai.

"Hade layukan waya da lambar dan kasa ta NIN da ake yi a yanzu kuma, an bullo da shi ne domin tabbatar da ganin tsarin tsarin rajistan layin wayan ya yi karko.

"Saboda haka ta yaya mutum mai hankali zai je ya wallafa irin wannan labarin," inji ta.

Uwa, ta kuma yi waiwaye ga barazanar hallaka Pantami da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi a baya saboda tsarin rajistar da rufe layukan waya marasa rajista da Ministan ya kawo.

"Ko dai har an manta barazar da Shekau ya yi masa ne, saboda Ministan ya birkita musu lissafi sun kasa ci gaba da harkokinsu yadda suka saba?"

Ko kafin NewswireNGR ta janye labarin na Daily Independent aka gano cewa shaci-fadi ne, Daily Independent din ta ambato wani hadimin Pantami -wanda ba ta bayyana sunansa ba- yana karyata rahoton a matsayin labarin kanzon kurege.

''Wannan yunkuri ne kawai na cin mutunci da kuma cin zarafin addinin da akidar mutum. Gwamnatin Amurka ba ta zargin sa da komai,'' inji hadimin Ministan cikin bacin rai.

Aminiya ta bi diddigi zuwa shafin Hukumar Bincike ta FBI ta kasar Amurka wadda aka ce tana neman Pantami; inda ta gano cewa babu ko da kalmar Pantami, ballantana wani mutum mai suna Isa Ali, ko Isa Ibrahim, a cikin jerin mutum 45 da FBI ta Amurka take nema ruwa a jallo kan zargin ayyukan ta'addanci a cikin kasar ko a kasashen duniya.

Kazalika a labarin na Daily Independent, ta ambato wani hadimin Pantami -wanda ba ta bayyana sunansa ba- yana karyata rahoton a matsayin labarin kanzon kurege.

''Wannan yunkuri ne kawai na cin mutunci da kuma cin zarafin addinin da akidar mutum. Gwamnatin Amurka ba ta zargin sa da komai,'' inji hadimin Ministan cikin bacin rai.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito Uwa , ta tana cewa, "an buga labarin ne da zummar bata sunan ministan.

"Ta ce wasu mutane ne da suka rasa yadda za su bullo wa Pantami domin su muzanta shi - shi ne suka fake da kirkirar labarin."

Kafin nada shi matsayin Minista, Pantami ya kasance shahararren mai wa'azin Musulunci, kuma ya dade yana caccakar ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram.

A shekarun baya, ya taba yin wata zazzafar mukabala tsakaninsa da shugaban Boko Haram na farko da jami'an tsaro suka kashe, Muhammad Yusuf, inda a mukabalar Pantami ya hana shi sakat da tambayoyi da kuma ruwan hujjjoji.

Bayan zamansa Minista, Pantami ya bullo da tsare-tsare da dama ta zummar dakile kafafen gudanarwa da kuma taimaka wa ayyukan ta'addanci.

Post a Comment

0 Comments