Ba Mu Da Lokacin 'Yan Tawaye, Ba Za Mu Tattauna Da Su Ba -Sabuwar Gwamnatin Chadi



Sabuwar Gwamnatin mulkin sojin Chadi ta ce ba za ta tattauna da 'yan Tawayen da suka kaddamar da hare-hare a yankin arewacin kasar ba makwannin da suka gabata wanda ma ake zargin su da kashe shugaban kasar Idris Deby Itno.

Wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, ta bayyana Kakakin gwamnatin sojin kasar Azem Bermandoa Agouna na cewa wannan ba lokaci ne na tattaunawa ba, kuma babu tattaunawar da za su yi da marasa bin doka.

Tun da farko, kakakin 'yan Tawayen Mahamat Mehdi Ali ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar a shirye suke su tattauna da gwamnati domin ganin an samo maslaha kan halin da kasar take ciki.

Post a Comment

0 Comments