Daga Muhammad Farouk Tsohon Daraktan hukumar tsaro ta DSS, Mike Ejiofor ya yi gargadi akan zaben 2023, idan ya ce idan har matsalar tsar...
Daga Muhammad Farouk
Tsohon Daraktan hukumar tsaro ta DSS, Mike Ejiofor ya yi gargadi akan zaben 2023, idan ya ce idan har matsalar tsaro a Nijeriya ya ci gaba da kazanta, to ba lallai a gudanar da zaben ba.
Mike Ejiofor ya bayyana hakan ne a yayin hirarsa da gidan Talabijin na Channels, a shirinsu na Sunrise Daily na ranar Litinin, inda ya nemi gwamnatin tarayya ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen kawo karshen matsalar tsaron da kasarnan ke fuskanta.
“idan ba a maida komai ya daidaita kafin shekarar 2023, idan har bamu gyara lamarin nan na mtsalar rashin tsaro da ake fuskanta a yankuna da dama na kasarnan ba, ina mai tabbatar muku da cewa ba za a gudanar da zabe ba”, ya tabbatar kamar yadda MADOGARA ta labarto.
Ya ci gaba da cewa; “za a yi rikici a kasarnan, rashin doka da oda zai balle. Akwai bukatar mu daidaita komai kafin 2023”, ya lurantar.
“mu fara magana akan wanzuwar kasarnan kafin ma a fara maganar zabe. Idan muka ci gaba a hakan, ba wani zabe da za a yi a 2023 saboda matsalolin da ake fuskanta”, ya nusasshe.
Ejiofor dangane da matsalar tsaron dake fuskantar kasarnan, ya ce akwai bukatar a duba kiraye-kirayen da jama’a suke yi na batun yiwa kasarnan kwaskwarima, wanda ya ce idan aka yi hakan, za a magance wadansu matsalolin.
Da yake magana dangane da zancen da ya fi daukar hankali a yanzu kuwa wato batun zargin da ake yiwa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, Mike Ejiofor ya ce babu yadda za a yi a ce DSS ba su binciki Pantami ba kafin a ba shi mukami a 2015. Inda ya bada misali da yadda DSS suka hana a tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC sakamakon rahoton da suka mikawa majalisar kasar.
“ba ni ne Kakakin DSS ba, amma ina mai tabbatar maka da cewa babu yadda za a yi a ce ba su bincike shi ba. Dole zai zama sun san yana goyon bayan Al-Qaeda da kuma sauran kungiyoyin ta’addanci. Amma idan SSS suka mika rahotonsu ga gwamnati, amma gwamnati ta ki amfani da rahoton, wa za a ga laifi?” ya tambaya.
No comments