Bani Da Wata Bukata Yanzu Kamar Haduwa Da Gwamna Zulum, Inji Mawaki Sani Tuwala


Daya daga cikin Mawakan Hausa a arewacin Nijeriya Yusuf Sani Abdullahi, wanda akafi sani da, Sani Tuwala ya yaba tare da jinjina ga Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum tare da Masa fatan Alkairi, kana kuma ya bayyana bashi da wani bukata a yanzu kamar ganin sa a gaban Gwamna.

Da yake magana kan matsalolin da ya fuskanta, Sani Tulawa ya bayyana cewa; "Ban taba haduwa da wani Gwamna ba tun lokacin da nake wakokina, amma yanzu bana bukatar ganin ko wani Gwamna kamar yanda nake bukatar ganin Gwamna Zulum, Inji shi.

"Duk Gwamnonin Nijeriya banga wanda yake da Kishin Kasar nan da al'ummarsa ba kamar Gwamnan Borno a yanzu, ba ruwansa da masu kai masa hari shi aiki kawai ya sani, kullum kuma yana cikin kai hari daga magauta amma bai tsayar da abunda yake yi ba."

"Dukkan Gwamnonin Nijeriya ba wanda yake tafiya kauyuka da yasan za'a iya kai masa hari harma da kokarin kisa amma shi kullum damuwarsa ya ga kansa a gurin tare da talakawansa, hakan kawai yasa naji ina matukar Kaunarsa, kuma ina son ganawa dashi.

Hajiya Ambassador Fateema Muhammad Gwani ta kasance itace tsani a garemu a tafiyar Jami'iyyar APC itama lallai muna jinjina ma irin kokarin da take yi a yankin Jihar Borno, haka ma Injiniya Mustapha Gubiyo Commissioner RRR, Borno, lallai shima yana taimaka mana sosai a Jihar Borno, haka ma mai gidanmu  Injiniya Yakubu Kasim, zonal technical aitel, north East, yana taka rawa sosai a tafiyar, Allah ya saka musu da Alkairi, amma dai burina yanzu kawai in gana da Gwamna Zulum.

Post a Comment

0 Comments