Lionel Messi da Frenkie de Jong da Griezman sune suka ci wa FC Barcelona kwallo kan Athletico Bilbao, inda suka lallasa su da ci 4 da ...
Lionel Messi da Frenkie de Jong da Griezman sune suka ci wa FC Barcelona kwallo kan Athletico Bilbao, inda suka lallasa su da ci 4 da 0 a wasan karshe na kofin Copa Del Rey.
Barcelona lashe wannan gasar shi ne ya ba su damar daukar kofi na farko a kakar wasa na bana.
Idan ba ku manta ba a cikin watan Janairun shekararnan, Athletic Bilbao ta lallasa Barcelona a kofin Super Cup da aka buga, wanda nasarar da Barcelona ta samu a wasan jiya kamar ramuwar gayya ce.
‘Yan wasan Ronald Koeman wanda suka kwashe shekaru biyu ba su dauki wannan kofin ba, sun zafafa a wasan sosai, inda De Jong ya fara samun nasarar jefa kwallo a raga daga bugun da Messi ya yi masa.
A wasan dai Messi ya zura kwallo biyu, sai kuma Antoine Griezmann ya zura kwallo daya.
No comments