Birtaniya Na Yi Wa Nijeriya Zagon Kasa A Yaki Da ‘Yan Ta’adda –Lai Mohammed

 


Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matakin da Birtaniya ta dauka na bai wa masu rajin kafa kasar Biyafara (IPOB) mafakar siyasa, cin mutunci ne ga Nijeriya a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin na Birtaniya zagon kasa da yakin da gwamnatin tarayya ke yi da ‘yan ta’adda ne, kuma hatsari ne ga tsaron Nijeriya.

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, a lokacin da suke tattaunawa da shi a shirin nan, NANForum, a ranar Talata a Abuja, inda Alhaji Lai Mohammed ya jaddada cewa matakin na Birtaniya ba abin yarda bane ga Nijeriya.

 “bari na fadi wannan kai tsaye, lamarin nan yana karkashin ikon ministan lura da harkokin wajen Nijeriya, ina mai tabbatar muku zai lura da hakan yadda ya kamata. Amma a matsayina na mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya, idan har rahoton cewa Birtaniya ta bai wa ‘yan IPOB da MASSOB mafakar siyasa ya zama gaskiya, to tabbas akwai matsala a wani wurin. Ganin cewa IPOB ba kawai haramta su aka yi ba, a’a amma sanya su a cikin jerin ‘yan ta’adda a Nijeriya, matakin na Birtaniya cin fuska ne ga Nijeriya a matsayin kasa:, ya tabbatar.

Alhaji Lai Mohammed ya ci gaba da cewa; “matakin na Birtaniya zagon kasa ne da yakin da kasarnan ke yi da ‘yan ta’adda, kuma cikas ne ga tsaron kasarnan. Matakin ba kawai ba daidai bane, ba zai yiwu ba su iya tabbatar da dalilansu na yin hakan ba:, inji shi.

Ministan ya ce a kwanakin nan an zafafa hare-hare kan hukumomin tsaro a Kudu maso gabashin kasarnan, inda ya ce kuma dukkanin hare-haren ana zargin ‘yan IPOB da yinsa ne duk da suna musantawa. “amma duk da haka a ce Birtaniya ta bai wa mabaratan ‘yan IPOB mafaka, abin a sanya alamar tambaya ne ga Birtaniya kan hakan. Idan zamu koma tarihi, abin da Birtaniya ta yi kamar a ce Nijeriya ce ta bai wa ‘yan IRA mafaka kafin yarjejeniyar zaman lafiya ta 1998 (1998 Good Friday Peace Agreement)”, inji shi.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ta labarto cewa; kasar ta Birtaniya ta fitar da tsarin yadda za ta bai wa masu rajin kafa kasar Biyafara mafakar siyasa. Inda a cikin tsarin bayar da mafakar ta siyasa, Birtaniya ta bayyana ‘yan IPOB a matsayin wadanda “ake zalunta” a Nijeriya, a daidai lokacin da kuma gwamnatin Nijeriya ta ayyana su a matsayin “’yan ta’adda”.

 


Post a Comment

0 Comments