Boko Haram Ba Su Shiga Damasak Ba, Karya Ne Labarin –Martanin Rundunar Soja

 

Janar Muhammad Yarima

Rundunar sojin Nijeriya ta musanta rahotannin dake cewa mutane fiye da dubu 100 sun tsere daga garin Damasak zuwa cikin Jamhuriyar Nijar, sakamakon farmakin mayakan Boko Haram.

Yayin tabbatar da rahotannin a ranar Alhamis, wani mazaunin garin Bulama Ahmadu ya shaidawa RFI Hausa cewar yanzu haka rabin mazauna garin na Damasak sun tsere domin tsira da rayukan su duk da kokarin da sojoji ke yi na hana su tafiyar.

Sai dai a yayin tashi zantawar da sashin Hausa na RFI, Daraktan yada labaran rundunar sojin Nijeriya Janar Muhammad Yarima, ya bayyana mamaki da takaici kan yadda rahoton da ya bayyana a matsayin na karya, ya samu karbuwa a wajen jama’a.

Janar Yarima ya ce mayakan Boko Haram ba su ma samu damar shiga garin na Damasak ba.

Bayanin daraktan rundunar sojin Najeriyar dai na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane dubu 65 suka fice daga garin na Damasak dake Jihar Barno domin tsira da rayukan su bayan hare haren da mayakan Boko Haram suka kai har sau uku cikin mako guda.

Babar Balock, kakakin hukumar kula da yan gudun hijira na Majalisar ya ce hare-haren sun tilastawa akalla kashi 80 na mazauna Damasak barin garin.


Post a Comment

0 Comments