Boko Haram Na Tsare Da Matasan Nijeriya Dubu Goma, Inji Gwamna Ortom

 

Daga Muhammad Farouk 

Gwamnan jihar Binuwe, Samuel Ortom ya tabbatar da cewa fiye da matasan Nijeriya dubu goma ne Boko Haram ke tsare da su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a a garin Makurdi a jawabin da ya gabatar a matsayin mai jawabi na musamman a taron da kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen birnin Tarayya Abuja suka shirya na 2021.

A cewar gwamnan, wadannan matasa da Boko Haram ta yi garkuwa da su sun hada da maza da mata, inda Boko Haram din ke ci gaba da wanke tunaninsu da kuma cusa musu akidarsu na yaki.

Ya kara da cewa; “manufar wadannan ‘yan ta’addan shi ne ci gaba da kashe-kashe, yiwa mata fyade, sace kayan al’umma, tada boma-bomai a wuraren gwamnati da na masu zaman kansu, wuraren ibada, fashi da makami da kuma garkuwa da jama’a”, inji shi.

 “wanda ya hada da sace matan Chibok (2012); Daliban makarantar Damasak (2015), da kuma daliban makarantar Dapchi (2018), ciki harda Leah Sharibu wanda har yanzu ana ci gaba da rike da ita”, inji shi.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwe ya ce rahoto ya nuna cewa Boko Haram na ci gaba da rike matasa maza da mata fiye da dubu goma; “kungiyar suke da alhakin kai hari a ofishin majalisar dinkin duniya dake Abuja. Sannan sun kashe mutum fiye da dubu talatin da kuma sanya miliyoyin mutane su rasa muhallansu”, ya tabbatar.

Ya karkare da cewa; “arewa maso gabashi babu tsaro ko kadan, sannan babu wata alamar cewa za a kawo karshen Boko Haram a nan kusa”, ya lurantar.

Post a Comment

0 Comments