Boko Haram Ta Hallaka Sojojin Nijeriya 31Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Nijeriya 31 bayan sun far musu a daidai lokacin da suke rakiyar wasu makamai, yayin da ‘yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin da ke jihar Borno.

A ranar Lahadi ne mayakan na ISWAP suka kai harin a agarin Mainok da ke wajen birnin Maiduguri, inda kuma suka kwashe makaman sojin.

Wannan harin shi ne mafi muni da aka kai wa sojoji a cikin wannan shekara.

Majiyar sojin kasar ta shaida wa AFP cewa, daga cikin dakarun da 'yan ta’addan suka kashe har da kwamandansu mai rike da mukamin Laftanar Kanar. 

An kaddamar da farmakin ne a lokacin da sojojin ke rakiyar makamai zuwa birnin Maiduguri kamar yadda majiyar tsaron ta tabbatar.

Mayakan sun iso ne a cikin manyan motoci da suka hada da masu sulke, inda suka bude wuta kan jami’an tsaron.

Rikicin Boko Haram ya kashe mutane akalla dubu 36 a Nijeriya tare da raba miliyan biyu da muhallansu a cewar alkaluman hukumomi.

Post a Comment

0 Comments