Bukin Cika Shekara 60 Da ‘Yancin Kai: Osinbajo Zai Wakilci Nijeriya A Kasar Sierra Leone

Daga Auwal Adam

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a ranar Talatarnan zai bar Abuja domin isa birnin Freetown domin halartar taron cika shekara 60 da samun ‘yancin kai da Sierra Leone ta yi. 

Mai taimakawa mataimakin shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Laolu Akande shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar A Abuja. 

Sanarwar ta ce Osinbajo zai wakilci Nijeriya domin haduwa da sauran shugabannin kasashen Afrika da ma duniya baki daya wadanda za su samu damar halartar taron. 

Bayanai sun ce alakar hulda tsakanin Nijeriya da Sierra Leone wata dadaddiyar alaka ce tun lokacin turawan mulkin mallaka. Kuma alaka ce ta fuskancin tattalin arziki, tsaro da sauran su na tsawon lokaci. 

Daga cikin tawagar mataimakin shugaban kasar, akwai karamin ministan harkokin wajen kasar, Ambassada Zubairu Dada, da sauran su. 

Ana sa ran zai dawo a daren yau Talata. 

Kasar Sierra Leone ta samu ‘yancin kanta ne daga Turawan mulkin Mallaka na Birtaniya a ranar 27 ga watan Afrilun 1961, kuma Milton Margai shi ne ya kasance Firaministan farko na kasar. 

Zaben farko da aka yi a kasar ya kasance ne a ranar 27 ga watan Mayun 1962. 

Inda Siaka Stevens ya kasance zababben Firaministan kasa a Mayun 1967.


Post a Comment

0 Comments