Cin Hanci Ba Zai Bar Najeriya Ta Cigaba Ba, Inji GandujeGwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ba za ta taba ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta.

Ganduje ya ce babu yadda za a yi kasar nan ta ci gaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a Najeriya.

"Za ku yarda da ci idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba," in ji Ganduje.

Ganduje ya bayyana hakan ne ya yin kaddamar da wani kwamitin na mutum takwas kan wasu dabarun yaki da rashawa a jihar.

An kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis da nufin rage cin hanci da kuma tabbatar da an gudanar da al'amura a bude a fadin jihar, in ji Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji.

-BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments