Wakilinmu
a Katsina ya labarto mana cewa saboda dalilan tsaro da ake fama da shi a jihar
ta Katsina, gwamnatin jihar ta haramta al'adar Tashe da ake yi cikin watan
Ramadana.
Hakan
ya fito ne a cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai da al'adu da harkokin
cikin gida Abdulkarim Yahaya Sirikathe ya fitar, wanda ya ce an dauki matakin
hakan saboda dalilai na tsaro kwanaki 15 da fara azumin.
Gwamnatin
jihar ta kuma umurci jami'an tsaro su kama duk wanda aka samu ya taka wannan
dokar.
0 Comments