Yayin da ake samu tsamin dangantaka tsakanin Musulmi da Kirstoci a wasu sassan Nijeriya, shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya ya gi...
Yayin
da ake samu tsamin dangantaka tsakanin Musulmi da Kirstoci a wasu sassan Nijeriya,
shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya ya gina masallaci domin bai wa al’ummar
Musulmi damar yin ibada a jihar Adamawa.
Masallacin
an gina shi ne a sansanin ‘yan gudun hijira a yankin da ake kira Sangere Margi
a garin Girei tare da gina gidaje 86 domin ‘yan gudun hijira da rikicin Boko
Haram ya raba su da muhallansu.
Bishop
Stephen Dami Mamza shi ne shugaban kungiyar kiristocin Nijeriya
reshen jihar Adamawa, ya kuma bayyana dalilan da ya sanya suka gina wannan
masallaci, inda ya ce; “akwai wadansu ‘yan gudun hijirar da nake kula da su,
akwai kirista akwai musulmi, mun gina musu gidaje 86 ga kuma mun gina musu, mun
gina makaranta, mun gina coci. Na gani bai dace kawai mu gina coci ma kirista
ba, musulmin da suna tsakaninsu ba su da yawa, amma na ce idan za a bar su su
gina masallaci da kansu zai dauke su lokaci kuma watakila zai gagare su, to shi
ne na ce ai suma ya dace a gina musu wurin da za su samu su yi ibada”, ya
tabbatar.
Gambo
Jika, shugaban kungiyar musulmi ta jihar Adamawa, ya nuna jindadinsa bisa
wannan, wanda ya ce hakan zai kara fahimtar juna tsakanin musulmi da kiristoci
a jihar. Inda ya kara da cewa tabbas hakan abin jindadi bane, abin kuma hada
zumunci ne.
No comments