Domin Murkushe ‘Yan Ta’adda Rundunar Soja Da Ta ‘Yan Sanda Za Su Hada Kai

 


Daga Muhammad Farouk 

A wani yunkurin kawo karshen ta’addanci da matsalar tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a Nijeriya, kwamitin tsaro na majalisar Nijeriya da Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya sun bayyana cewa sun samar da alakar aiki tsakanin sojoji da 'yan sandan kasar wanda hakan zai kara musu kwarin guiwa da taimaka musu wajen murkushe matsalar tsaron da ake fama da ita  a kasarnan.

Rundunar sojin ta bayyana hakan ne a sanarwar da Kakakinta, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar dangane da ziyara ta musamman da kwamitin tsaro da kuma Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sanda suka kai wa Shugaban rundunar sojin kasar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.


Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana cewa lallai ya ji dadin wannan ziyara domin ta zo ne a daidai lokacin da yake da bukata, domin a cewarsa dama akwai bukatar tattaunawa a tsakanin kwamitin da rundunar sojin kasar da ta 'yan sanda domin samar musu da kayan aiki da kara musu kwarin gwiwa na aiki wanda hakan zai taimaka musu wajen tunkarar matsalar tsaron kasarnan.

Wannan dai ita ce ziyarar mukaddashin Babban Sufeton 'yan sanda Usman Alkali Baba ta farko tun bayan nadin da aka yi masa, ya ce tabbas hakan zai taimaka a kawo karshen matsalar 'yan fashin daji da ta sauran muggan ayyuka da ke addabar kasar.

Mukaddashin Babban Sufeton ya kara da cewa hadin kai tsakanin bangarorin biyu na da amfani ganin cewa duka al'ummar kasar sun dogara ne a kansu wajen tabbatar da tsaro.

Yayin wannan ziyara shugaban kwamitin tsaro na majalisar kasar Sanata Mohammed Ali Ndume da wasu manyan jami'ai sun tofa nasu albarkacin bakinsu.
Post a Comment

0 Comments