Duk Matashin Da Ya Amince Da Allurar Rigakafin Korona Za A Biya Shi Naira Dubu Arba'in


Rahoton BBC HAUSA

Wata jiha a Amurka ta ce za ta bai wa matasa tukwicin dalar Amurka 100 kwatankwacin kimanin naira dubu arba'in idan suka amince aka yi musu allurar rigakafin korona.

Jihar West Virginia ta ce tana fatan ba da tukwicin ga yan shekara 16 zuwa 35 domin basu kwarin gwiwar zuwa a yi musu allurar.

A cewar gwamnan jihar, Jim Justice, matasa suna da rawar takawa a yaƙi da annobar ta korona.

Jihar tana daga cikin jihohin Amurka da aka tsara yi wa jama'a da yawa allurar rigakafin sai dai lamarin ya fuskanci tsaiko a baya-bayan nan.

Akwai fargabar cewa matasa na iya nuna rashin damuwa da zuwa yin rigakafin.

Ba da kudin na nufin mutanen da aka yi wa allurar da ke cikin rukunin za su iya samun dalar Amurka 100 da riba a wani lokaci nan gaba.

Za kuma a bai wa duk wanda shekarunsa suka kai 16 zuwa 35 da tuni aka yi musu allurar.

West Virginia ce jihar da ta fi yawan masu cutar korona a Amurka a cewar Jaridar New York Times.

Kashi 52 cikin 100 na mutum miliyan daya da rabi sun yi allurar sau ɗaya a cewar Gwamna Justice amma ya kara da cewa wasu kashi 40 na al'ummar jihar na iya yin baya-baya wajen zuwa a yi musu rigakafin.

Post a Comment

0 Comments