Duk Sukar Da Za Ku Yi Min Ba Zan Yi Sulhu Da ‘Yan Ta’adda Ba –El-Rufai

 


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya mayar da martani kan wani tsohon bidiyo da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta wanda ke nuna shi yana sukar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kan ƙin biyan kuɗin fansa don kuɓutar da ƴan matan Chibok.


Gwamnan ya ce an naɗi bidiyon ne a shekarar 2014 bayan sace ɗaliban makarantar ta Chibok, wanda kuma ya ke zargin Jonathan da rashin sanin aikinsa sannan ya buƙaci ya bi duka hanyoyi wajen ganin an kuɓutar da ƴan matan ko da kuwa tattaunawa ce da mayaƙan Boko Haram.


Sai dai wata sanarwa da aka fitar mai ɗauke da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai bai wa gwamna El-Rufa'i shawara kan sadarwa, ta ce tun daga shekarar 2014 kawo yanzu, salon da ƴan bindiga suka ɗauka ya sauya.


Kuma shi ya sa a yanzu El-Rufa'i ba ya goyon bayan biyan kuɗin fansa ko tattaunawa da ƴan bindiga.


Sanarwar ta ce masu yada bidiyon ba su yi la'akari da halin tashin hankalin da gwamnan da al'ummar jihar Kaduna suke ciki ba, amma suke sukar El-Rufa'i don ya jaddada manufarsa ta son bin doka da ƙa'ida na ƙin son biyan kuɗin fansa da yin sulhu da ƴan bindiga.


Haka kuma, sanarwar ta ce idan aka yi la'akari da jerin sace-sacen mutane da ɗalibai da suka auku a Najeriya a shekarun nan, ana iya fahimtar cewa biyan kuɗin fansa da yin sulhu ba su ne za su kawo ƙarshen matsalar ba, illa ma dai su ƙara wa maharan ƙarfi.


Sanarwar ta ce duk da cewa matsalar tsaro ta yi wa Najeriya dabaibayi, bai kamata a biye wa ƴan bindigar ba wajen ba su kuɗin fansa wanda suke samu su sai makamai.


A watan Maris ne ƴan bindiga suka sace ɗalibai daga wata makarantar gaba da sakandire a unguwar Mando a jihar ta Kaduna kuma suka buƙaci a biya kuɗin fansa don sako ɗaliban amma kawo yanzu gwamnatin jihar ba ta biya kuɗin ba don haka suna hannun ƴan bindigar.


Haka kuma, a farkon wannan watan na Afrilu ma an sace wasu ɗalibai daga jami'ar Greenfield duk a jihar ta Kaduna kuma kawo yanzu masu garkuwan sun kashe biyar daga cikin ɗaliban.


Gwamna Nasir El-Rufa'i dai ya daɗe yana bayyana cewa bai amince da sulhu da biyan kuɗin fansa ba ga ƴan bindiga. Ya ce kamata ya yi a kawo ƙarshensu da ƙarfin tsiya ta hanyar yin fito na fito da jami'an tsaro.

-Rahoton BBC Hausa


Post a Comment

0 Comments