Shugaba Muhammadu Buhari Daga Muhammad Farouk Kungiyar kiristoci ta Nijeriya ‘The Pentecostal Fellowship of Nigeria’ ta zargi fadar ...
![]() |
Shugaba Muhammadu Buhari |
Daga Muhammad Farouk
Kungiyar kiristoci ta Nijeriya ‘The
Pentecostal Fellowship of Nigeria’ ta zargi fadar shugaban kasa da boye gaskiyar
bayanai a kan rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban kungiyar ta PFN, Bishop
Wale Oke, ya bayyana hakan ne a Legas a yayin da yake ganawa da kafafen watsa
labarai. Ya kuma koka a kan yadda Buhari ya zabi ya rika zuwa kasashen waje
neman a duba lafiyarsa maimaikon shugaban ya tsaya ya gyara asibitocin cikin
Nijeriya.
Oke har wala yau ya nemi gwamnatin
tarayya da ta rika bayyana gaskiya akan rashin lafiyar Buhari saboda a cewarsa
hakan ne zai sanya a matsayinsu na kiristoci su san yadda za su yi shugaba
Buhari addu’ar samun lafiya.
“muna yiwa shugaban kasa addu’ar samun koshin
lafiya; ya bar kasarnan na fiye da mako biyu kan neman lafiya. Abubuwa biyu ya
sanya muka damu da halin da shugaban kasa ke ciki. Mun yadda cewa ba a fadawa
kasarnan gaskiya kan rashin lafiyarsa. Muna neman gwamnatin tarayya da fadar
shugaban kasa da su baza faifai a kasa su gaya mana me ke damun shugaban kasa. Yanzu
shi mutum ne na kowa, akwai bukatar mu san yadda zamu yi masa addu’a. A daina
boye mana batun rashin lafiyar shugaban kasarmu, a gaya wa kasar halin da yake
ciki domin mu san yadda zamu yi masa addu’a”, inji shugaban kungiyar kiristoci
ta PFN.
Kungiyar ta nuna damuwa sosai na
yadda ake kai shugaba Buhari kasashen waje domin a duba lafiyarsa, wanda suka ce hakan babbar
barazana ce; “wannan yana nufin shugaban kasarmu ya fi samun aminci a hannun
Turawa fiye da hannunmu? Idan wadannan mutane suka yi masa wani abu, me zamu yi
ke nan”, suka tambaya.
A karshe ya koka yadda sauran
shugabannin Nijeriya suma suke garzayawa kasashen waje da zarar sun ji yanayin
rashin lafiya, inda ya ce a maimaikon su rika yin hakan, akwai bukatar su sanya
kudin a bangaren lafiya domin bunkasa bangaren.
No comments