Gidauniyar MMAWT Ta Biya Wa Fursunoni Tara A Sakkwato


Daga Wakilinmu

Shugabar Gidauniyar MMAWT Legacy kuma matar Gwamnan jihar Sakkwato, Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal, ta biya wa wasu fursunoni su biyar kudin tara da aka yanka musu, domin murnar shigowar watan Ramadan.

Matar Gwamnan ta samu wakilcin Hajiya Laraba Dattijo da kuma babbar mai baiwa Gwamna shawara kan ilimin ya'ya mata, Hajiya Aisha Maina.

A sakon ta na fatar alhairi matar gwamnan ta yi kira ga wadanda suka amfana da su kiyaye komawa cikin dabi'un da suka kawo su gidan gyaran halin tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba. 

Matar Gwamnan ta baiwa dukkan wadanda aka saka Naira dubu goma (10,000) tare da alkawarin karin tallafi zuwa gaba. 


Babban jami'i mai kula da gidan yarin, ya yi alkawarin kammala dukkan takardun sakin na su kamin ƙarshen mako. 

Gidauniyar MMAWT legacy, ta jima tana tallafawa domin samarwa fursunoni saukin rayuwa da kuma tallafawa wadanda aka saki.

Post a Comment

0 Comments