Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamna Bagudu Na Kebbi Ya Taya Ministan Shari'a Malami Murnar Cika Shekara 54

Daga Zaharaddeen Abbas  Sabanin rahotannin da ake yadawa akan cewa ministan shari'a kuma babban mai shigar da kara na gwamna...


Daga Zaharaddeen Abbas 

Sabanin rahotannin da ake yadawa akan cewa ministan shari'a kuma babban mai shigar da kara na gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami, an kwantar da shi a asibiti, sai dai a shekaranjiya Juma'a ministan ya shiga ofishinsa bayan ya dawo Nijeriya daga ziyarar aiki da ya kai kasar waje harma ya tattauna da mukaddasar Darakta a bangaren sanin dokokin al'umma, Mrs Maimuna Lami Shiru. 

Abubakar Malami ya cika shekara 54 a duniya, inda ya karbi bakuncin gwamnan jiharsa, Sanata Atiku Bagudu wanda ya kai masa ziyara domin taya shi murnar cika shekara 54 a duniya. 

A ranar Litinin din 12 ga watan Afrilun 2021, Abubakar Malami a yayin da yake gabatar da jawabi akan maudu'i mai taken; 'Justice Dispensation in Nigeria: Navigating Through Thorny Terrain’, ya bayyana cewa dukkanin wadanda suka rike Mukamin AGF sai da aka nemi tozarta su a kokarinsu na gudanar da ayyukansu. 


Malami ya ce dole ne mai mukamin AGF ya fuskanci matsaloli da kalubalen a tafiyarsa a yayin da yake kokarin gudanar da ayyukan da suka doru a kansa. 

Kamar da kasa, sai rahotanni suka bayyana cewa AGF Malami Abubakar ya yanke jiki ya fadi, jim kadan da kammala jawabinsa a Sakkwato. Inda aka bayyana cewa an kwantar da shi a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja bayan ya bayyana gaban taron majalisar zartaswa na tarayya a ranar Laraba.  

Sai dai a bayanin da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai da hulda da jama'a ya fitar, Dr Umar Jibrilu Gwandu, ya bayyana cewa ministan na nan cikin koshin lafiya. 

Kuma Dr Gwandu ya tabbatar da cewa har wala yau Ministan ya karbi bakuncin Sanata Aloysius Etok a ofishinsa bayan tattaunawa da Daraktar sanin dokokin al'umma. 

No comments