Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamna Bala Muhammad Ya Biya Kudaden Jarabawar NECO Da JAMB

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da biyawa dalibai dubu uku da dari takwas da goma da suka ci ...


Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da biyawa dalibai dubu uku da dari takwas da goma da suka ci jarabawar share fagen SSCE da matakin A da B.

Hakan ya fito ne a sanarwar da Lawal Muazu Bauchi, mai tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani ya fitar a ranar Alhamis 15 ga Afrilun 2021.

Har wala yau Gwamnan ya amince da biyan NABTEB wa dalibai dubu da dari bakwai da hamsin da daya dake aji shida a makarantun fasaha dake jiha da kuma kudin NBAIS wa dalibai dari hudu da casa'in da tara a kwalejojin horas wa kan harshen larabci na gwamnati.  

Kimanin Naira miliyan dari da tamanin da biyar da dubu dari biyar da tamanin da dari biyar da hamsin aka ware don biyan kudaden rajistar kuma ya zuwa yanzu babu wata cibiyar jarrabawa dake bin gwamnati bashin kudi inda gwamnan ya bada umurnin biyan sabbin kudaden rajistar kafin watan Agustan wannan shekara.

A cewar kwamishinan ilimi na jihar Dakta Aliyu Tilde ya zama wajibi ga dukkanin daliban da aka biya wa rajistar wadannan jarabawa su gaggauta yin rajistar neman katin dan Kasa domin cike fom din da ya ce cur da cur za a yi wato ganin Annabin tsohuwa.

Dakta Tilde ya ce gwamnatin Sanata Bala Muhammad ta shirya tsaf don tabbatar da wanzuwar sabbin dabarun inganta ilimi da suka dace da zamani don gina rayuwar shugabannin gobe wato matasa.

No comments