Gwamna El-Rufai Zai Rushe Kasuwar Panteka Da Dubban Daruruwa Ke Amfana


Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya shirya tsaf domin rushe kasuwar Panteka, inda  ya ba su wa'adin kwana bakwai ko 'yan kasuwar su tattara kadarorinsu daga kasuwar. 

Gwamnatin Kadunar na wannan rushe-rushen ne a tsarin raya birane da habaka su ta jihar Kaduna, inda gwamnatin za ta rushe tsohuwar kasuwar Panteka mai shekaru 60 da kafa ta. 

 Gwamnatin dai ta bukaci 'yan kasuwar su tashi a cikin lokacin da aka ba su ko kuma ta rushe kuma su rasa dukiyoyinsu dake ciki. 

Kasuwar Panteka din dake kusa da makarantar Foliteknik ta Kaduna, yanzu haka dai za su tattara komatsansu su barin wurin. 

Hukumar tsari da habaka birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ita ce ta ba su wannan wa'adin na kwana bakwai a cikin takardar da aka raba a Juma'ar da ta gabata. 

A wata takarda da darakta janar na KASUPDA yasa hannu kuma ya fitar, Isma'ila Dikko, yace "A cikin tsarin gyara birane na gwamnatin jihar Kaduna, an baku wa'adin kwana 7 daga ranar da kuka samu takardar nan da ku tashi tare da kwashe dukkan kayanku daga wurin", inji shi.

Ya ci gaba da cewa; "rashin biyayya ga wannan umarnin zai sa hukuma ta kwace dukkan kayanku tare da rushe ginin a lokacin da wa'adin ya cika kamar yadda sashi na 60, sakin layi na 2 ya tanadar", ya jaddada.

Tun farko dai, jama'a da dama ciki harda tsohon shugaban makarantar dake makwabtaka da kasuwar, Farfesa Muhammad Idris Bugaje, ya roki gwamnan da ka da ya rushe tsohuwar kasuwar, a madadin haka, ya mayar da ita wurin tarihi saboda dadewarta.

Tsohuwar kasuwar Panteka ta kwashe shekaru bila adadin inda ta kasance wurin siyar da sassan ababen hawa har da jiragen sama wanda makera ke hadawa. 

Post a Comment

0 Comments