Gwamnan Zamfara Ya Bai Wa Fulani Mukamin Mataimaki Na Musamman


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na tafiya da kowa da kowa, yanzu haka a karkashin ofishin Matar Gwamna, Hajiya Aisha Bello Matawallen Maradun, Fulani 20 ne suka samu mukamin mataimaka na musamman na Gwamna Bello Matawalle daga kungiyar Miyatti Allah.
 
Sakatariyar yada labaran ta matar gwamna, Zainab Shuaib Abudullahi ce ta bayyana haka a takardar da ta sanya ma hannu ta kuma rabawa manema labarai a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

A cewarta, da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, shugaban kungiyar na jihar ta Miyatti Allah Alhaji Tukur Abubakar ya jinjinawa  wa matar gwamna a kan kokarinta na samar da canji mai ma’ana ga Fulanin da sauran al'ummar jihar Zamfara.

Abubakar ya nuna matukar godiyarsa ga Gwamna Bello Matawalle saboda goyon bayan da yake baiwa Fulanin tare da saka su cikin gwamnatinsa.

Kuma ya ba da tabbacin cewa, kungiyar ta Miyatti Allah za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya da hadin kai don nasarar gwamnatin Matawalle da ci gaban jihar.

Post a Comment

0 Comments