Gwamnatin tarayya ta fara biyan wadanda ta dauka aiki na musamman a shirinta na ‘ Special public works (SPW)’. Festus Keyamo,...
Gwamnatin tarayya ta fara biyan
wadanda ta dauka aiki na musamman a shirinta na ‘Special public works
(SPW)’.
Festus Keyamo, karamin ministan
kwadago ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.
Shirin na SPW shiri ne da gwamnatin
tarayya ta bullo da shi kuma ya fara aiki a watan Yulin 2020 inda ta dauki ma’aikata
dubu dari bakwai da saba’in da hudu aiki (774, 000) domin gudanar da wani aikin
zango a fadin Nijeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
amince da a fara biyan kudaden a wani mataki na rage radadin asarar da cutar
korona ta haifar.
A cikin watan Maris din 2021 ne,
Keyamo ya ce shugaba Buhari ya bada izinin a fitar da kudaden domin fara biyan
wadanda suka amfana da shirin.
Ya ce bayan sakar wadansu ba’adin
kudaden ne ga ma’aikatar kudi domin biyan wadanda suka amfana da shirin SPW
din, minista Keyamo ya ce sai ya bayar da umurnin fara binciken asusun wadanda
za su amfana da kudaden kafin fara biyansu.
“mun gano wadansu asusun ba su hada shi da
lambar sirri na asusun su ba (BVN), wasu kuma sunayen na su ba iri daya bane da
lambar BVN dinsu, wasu kuma ba su da BVN”, inji shi.
Ministan ya ce a wani mataki na
kawar da rashawa a harkar, ya bukaci Cibiyar horas da ayyuka ta kasa, NDE da su
rubuta wasika zuwa ga bankuna domin a gudanar da bincike kafin fara biyan
kudaden.
“ya zuwa yanzu Bankin ACCESS ne
kawai suka tabbatar da ingancin asusun, inda a yau (Asabar) NDE suka fara biyan
kudaden ga wadanda suke da asusu da Bankin ACCESS”, ya tabbatar.
Ya ce sauran bankunan da ya hada da
ZENITH, UBA, FCMB, FIDELITY, HERITAGE da Yobe Micro-Finance Banks ana kan
bincike.
No comments