Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Sace Daliban Jami'a A Jihar


Daga Muhammad Farouk

Kwamishinan lura da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da cewa a daren jiya Talata ne ya samu kira cewa wadansu 'yan bindiga sun kai hari Jami'ar Greenfield dake kauyen Kasarami  dake karamar Hukumar Chikun a titin Kaduna zuwa Abuja. 

Kwamishinan ya ce rundunar 'Operation Thunder Strike (OPTS)' da sauran jami'an tsaro suka yi maza suka kai dauki a Jami'ar amma a lokacin 'yan bindigar sun gudu. Kamar yadda Kwamishinan ya tabbatar a sanarwar da ya fitar a yau Laraba. 

Ya tabbatar da cewa bayan sun yi bincike sai suka tarar da gawar daya daga cikin ma'aikatan Jami'ar mai suna Paul Ude Okafor da aka kashe, a yayin da aka yi awon gaba da dalibai da dama. 

Samuel Aruwan ya ce sauran daliban da suka rage, jami'an tsaro sun lura da su a inda suka mika su ga makarantar da misalin karfe 12 na ranar yau Laraba 21 ga watan Afrilun 2021. 

Sai dai Kwamishinan ya ce hakikanin adadin wadanda aka sace ba a kai ga tantancewa ba. 

Sai dai ya ce tuni aka baza Jami'an tsaro a yankin domin bada tsaro, inda ya yi alkawarin cewa za a sanar da al'umma duk nasarar da aka samu.  

Post a Comment

0 Comments