Gwamnatin Kano Ta Kulle Kwalejin Fasaha Ta Bagauda Saboda Matsalar TsaroGwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta Kano ta bada umurnin a kulle Kwalejin Bagauda da gaggawa. 

Gwamnatin ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Aliyu Yusuf, Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi a Kano ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai. Inda ya ce Kwamishinan ilimi a jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa'id Kiru ne ya bada umurnin sakamakon rahotanni masu ban tsoro daga hukumomin tsaro na bukatar da yake akwai na kare rayukan dalibai, Malamai da sauran ma'aikatan Kwalejin. 

Ya kuma nemi iyaye da su yi azamar kwashe 'ya'yansu daga Kwalejin ba tare da bata lokaci ba. 

A don haka Kwamishinan ya yi amfani da wannan damar wajen mika godiya ga gwamnatin jihar da kuma Iyaye bisa goyon baya da suke bai wa tsare-tsaren gwamnati musamman akan abin da ya shafi tsaro. 

Post a Comment

0 Comments