Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Tsarin Karantarwa A Makarantun Allo Kwaskwarima


Majalissar zartarwa ta Jihar Katsina ta amince da gyaran dokar da ta kafa hukumar kula da ilimin addinin Musulunci kamar yadda LEADERSHIP A YAU ta labarto.


Wannan zai ba da damar dora mata alhakin dubawa da kuma kula da makarantun allo a jihar.


Mai ba gwamna shawara na musamman a kan samar da guraben ayyukan yi Alhaji Hussaini Adamu Karadua ya bayyana haka bayan fitowa daga taron majalissar zartarwar jiha wanda Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranta.


Alhaji Hussaini Adamu Karaduwa wanda ya jagoranci wani kwamiti na musamman domin tantance makarantun allo a jihar nan, haka kuma, ya ce taron ya amince a mayar da almajiran da ba ‘yan asalin jihar nan ba zuwa garuruwansu na haihuwa.


Kamar yadda ya ce daga cikin almajirai 7,893 da aka gano, guda 2,052 sun fito ne daga jamhuriyyar Nijer, yayin da sauran ‘yan asalin jihar Katsina ne tare da wasu da suka fito daga sauran jihohi.


Ya ce amincewa da mayar da almajiran zuwa garuruwansu na asali da kuma yin kwaskwarima na dokar na daga cikin shawarwari ne na kwamiti na musamman da ya jagoranta wanda aka gabatar lokacin taron majalissar zartarwa ta jiha.


A halin da ake ciki kuma, majalisar zartarwa ta jiha ta amince da ayyukan shawo kan zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da zasu lakume sama na Naira Miliyan Dubu Ukku.


Kwamishinan muhalli Alhaji Hamza Suleiman ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ma manema labarai jawabi bayan kammala taron majalissar zartarwar jiha.


Post a Comment

0 Comments