Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Kaji 329,000 A Gidajen Gona 62Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kashe kaji sama da 329,000 a cikin gidajen gona 62 a fadin kasar, biyo bayan wata cuta da ake alakantawa da murar tsuntsaye, wadda kuma ke ci gaba da yaduwa a kasar tun bayan bullarta a ranar 29 Janairu kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Alkaluma sun nuna cewa daga watan Janairu da cutar ta bulla zuwa ranar 5 ga watan Afrilu akwai tsuntsaye 421,947 da suka kamu da wannan cuta, yayin da 92,422 suka mutu dalilin cutar, wadda yanzu ta bulla a kananan hukumomi 20 a jihohi takwas na kasar.

Wata majiya daga ma'aikatar noma ta ce a ranar 9 ga watan Afrilu da muke ciki ne aka kashe kaji 329,556 a gonaki 62.

A ranar 29 ga watan Janairu ne Daraktan da ke lura da harkokin dabbobi Dakta Adeniran Alabi, ya tabbatar da bullar cutar a yankin karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano a arewacin Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments