Gwamnatin Zamfara Ta Cafke Jami'an Tsaro Bakwai Da Suke Taimakawa 'Yan Bindiga A Jihar

       Bello Matawalle, Gwamnan Zamfara


Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cafke jami'an tsaro guda bakwai da suke taimakawa 'yan bindiga a jihar da sauran jihohin arewa maso yamma. 

Gwamnatin ta Zamfara ta zargi jami'an da yiwa ayyukan soji a jihar kutungwila, inda suke bai wa 'yan bindigar bayanan sirri na ayyukan sojin, ba su makamai, harsasai da kuma kayan sojoji. 


Da yake ganawa da manema labarai a Gusau, kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Dosara ya ce; wadanda ake zargin a yayin da ake bincikensu, sun tabbatar da laifin da ake zarginsu da shi. 

"Jami'an 'yan sanda bisa amfani da dabaru na bayanan sirri, sun kama wadansu jami'an tsaro da ake zarginsu da zagon kasa ma ayyukan sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da 'yan bindiga da suka addabi jihar da ma yankin da ta'addanci", inji shi. 

Ya ci gaba da cewa; ina son sanar muku cewa; gwamnatin jihar ta samu rahoto daga 'yan sanda cewa an kama jami'an tsaron bakwai da ake zarginsu da tallafawa 'yan bindigar a fadin jihar", ya tabbatar. 

Ibrahim Dosara ya ce yiwa yaki da 'yan bindigar zagon kasa da wadansu jami'an tsaron ke yi yana daga cikin abin da yake kawo wa yakin koma baya. Ya kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargi, tuni aka mika su ga hukumomin tsaron da suka dace domin daukar mataki na gaba. 

Post a Comment

0 Comments