Har Yanzu 'Yan Nijeriya Ba Su Da Jam'iyyar Da Ta Wuce APC, Cewar Sakataren Jam'iyyar

Daga Muhammad Farouk

Sakataren kwamitin riko na jam'iyyar APC ya tabbatar da cewa har yanzu 'yan Nijeriya sun fi amincewa da jam'iyyar ta APC duk da kulen da ake fuskanta a kasar.

Sanata James Akpanudoedehe, wanda yake shi ne Sakataren riko na jam'iyyar shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a Abuja a yayin kaddamar da Kwamitin ci gaba da rijistar 'ya'yan jam'iyyar. 

Sanata Akpanudoedehe ya ce kwamitin ya sanya lura da yadda aka rika Rijistar 'ya'yan jam'iyyar a duk fadin kasar, wanda ya ce tabbas an samu gagarumar nasara. 

Akpanudoedehea ya kara da cewa; 'yan Nijeriya tabbas ba su da jam'iyyar da ta wuce APC, a don haka ne ma suka yarda da ita. 

"Gaskiya ne cewa annobar cutar korona ya yi mana illa sosai, kamar yadda ya yi wa tattalin arzikin sauran manyan kasashen duniya illla. Gwamnatin APC ta tunkari abin yadda ya kamata", inji shi. 

Sanata Akpanudoedehe ya ce gwamnatin APC ta tallafa sosai ga kananan 'yan kasuwa da matsakaita da kuma marasa galihu wanda korona ta illatawa tattalin arziki. 

Akpanudoedehea ya ce kuma har yanzu gwamnatin APC na yin hakan. 

Post a Comment

0 Comments