Hare-haren Boko Haram: Muna Cikin Tashin Hankali A Yobe, Inji Gwamna Mai Mala Buni


Rahoton BBC HAUSA

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya ce suna cikin tsaka mai-wuya sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram da suka tada musu hankali tun ranar Juma'ar makon da ya gabata.

Mai Mala ya ce sanin kowa ne halin da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sai dai hare-haren da suke gani a yanzu na tada hankula matuka kuma ya zama dole a tunkare su.

A tattaunawarsa da BBC, gwamna ya ce a baya komai ya yi sauki amma a wannan lokaci abin ya tsananta, saboda ba a san dalilan mayakan ba, kuma zuwansu na wannan lokaci ya sha bamban da wanda aka saba gani a baya.

Kalaman gwamna na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa cewa ba a ji komai daga gareshi ba tun da mayakan suka farwa garin suna kashe mutane da tilastawa daruruwa tserewa.

Daruruwa sun ce sun tsere ne saboda gudun kada a ritsa da su a musayar wutar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram, ko da yake akwai masu cewa da dama sun mutu.

Sai dai gwamnan ya shaida wa BBC cewa ba a zaune yake ba, a lokacin zantawarmu da shi yana mai tabbatar da tattaunawa da hafsoshin tsaro a Abuja domin laluben mafita.

Ya ce, "Dama mayakan kan shigo jifa-jifa su wawushe kayan abinci da dukiya sai dai a wannan lokaci har kwana suka yi cikin gari.

Mutanen garin sun shiga ɗimauta da yanayi na tashin hankali, wannan dalili ya tilasta musu tserewa domin neman mafaka a garuruwa makwabta.

Ina tattaunawa da babban hafsan tsaron Najeriya domin neman hanyoyin dakile mayakan, kuma yanzu haka garin ya dawo karkashin jami'an tsaro", in ji Mai Mala Buni

Amma gwamnan ya nuna damuwarsa matuka inda yake cewa su a matakin jihar suna iya ƙoƙari domin ganin an samu saukin wannan al'amarin.

A baya-bayan nan dai ƙungiyar Boko Haram ta zafa-zafa hare-harenta a Geidam da wasu garuruwan arewa maso gabashin Najeriya.

Daga cikin waɗanda fafatawar ranar Juma'a ta ritsa da su har da wata mata da ta mutu sanadin wani makamin roka da aka harba gidan surukunta, inda ta je ziyara a Geidam.

Majiyoyin sun ce mayakan sun kuma fasa shaguna da dama, kana suka yi awon gaba da kayan abinci mai yawa.

Haka zalika, an fafata tsakanin 'yan Boko Haram da sojoji a garin Mainok na jihar Borno mai maƙwabtaka, har wasu rahotanni na cewa harin ya ritsa da wasu sojoji.

Jaridar intanet ta PRNigeria ta rawaito cewa sojoji sun katse hanzarin 'yan Boko haram ɗin da suka kai harin a Mainok ta hanyar yi musu lugudan wuta ta kasa da sama.

Yayin da wata majiya ta daban kuma ke cewa an kashe wasu sojoji har an yi awun gaba da kayan aikinsu.

Sai dai duk kokarin da na yi na ji daga kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Muhammad Yarima abin ya ci tura.

Matsalar tsaro dai a Najeriya na sake rincaɓewa abin da ya sanya masu sharhi ke fargabar makomar ƙasar nan gaba musamman zargin da ake cewa sojojin ƙasar na fuskantar ƙarancin makamin yaƙi da mayakan da ke dagula lamuran tsaro a ƙasar.

Post a Comment

0 Comments