Harin Boma-bomai Ya Hallaka Mutum Hudu Da Raunata 12 A Pakistan

 


Wata mota da aka shaketa da boma-bomai aka kuma ajiyeta a bakin Otel din da Jakadan kasar Chana a Pakistan ke zaune a kudu maso yammacin birnin Pakistan na Quetta ta kashe mutum hudu da kuma raunata mutum 12 kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar kamar yadda MADOGARA ta labarto.

Quetta shi ne babban birnin yankin Balochistan, iyaka da kasar Afghanistan. Kuma yankin ya kwashe gomomin shekaru yana fama da hare-haren ta’addanci daga wadanda suke son ballewa daga kasar ta Pakistan bisa dogaro da cewa hukumomin Pakistan din na amfana da dimbin arzikin da yake kumshe a yankin na su.

Harin bom an kai shi ne a gaban Otel din Serena a daren ranar Laraba, inda hukumomin tsaro tuni suka dukufa wajen bincike a wurin da bom din ya tashi kamar yadda Muhammad Akran, daya daga cikin masu aikin ceto a wurin ya tabbatar da gidan Talabijin na CNN.

Otel din na Serena ana bayyana shi a matsayin Otel mafi tsaro a birnin Quetta din, sakamakon yadda jami’an huldar Jakadanci da na diflomasiyya da jami’an kasashe daban-daban ke zama a Otel din idan sun kawo ziyara.

Shaidun gani da ido sun ce harin na bom din ya auku ne bayan an sha ruwa a daidai lokacin azumin watan Ramadana. “an ajiye motar bom din ne cikin inda ake ajiye motoci”, inji ministan  cikin gida na yankin Balochistan, Ziaullah Lango kamar yadda Reuters ta labarto. “daya daga cikin jami’an ‘yan sandan mu na daga cikin wanda suka samu rauni”, ya tabbatar.

‘Yan ta’addan Pakistan da aka fi sani da Tehreek e Taliban Pakistan (TTP) sun dauki alhakin kai harin a sakon Imel da gidan Talabijin na CNN suka ce sun samu daga Kakakin kungiyar TTP, Muhammad Khurassani wanda ya ce harin na kunar bakin wake ne suka kai.

Ambasadan kasar Chana a Pakistan, Nong Rong, yana zaune ne a Otel din, amma ba ya nan lokacin da aka kai harin bom din kamar yadda ministan lura da harkokin cikin gida na Pakistan,  Sheikh Rashid Ahmad ya tabbatar a ranar Laraba ga kafar watsa labarai na Reuters.

 

Post a Comment

0 Comments