Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Hisbah Ta Cafke Balagaggu Sha Daya Ba Sa Azumi A Kano

Daga Wakilinmu Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar kama mutum goma sha daya da ba sa azumin watan Ramadan a ranar Alhamis....


Daga Wakilinmu

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar kama mutum goma sha daya da ba sa azumin watan Ramadan a ranar Alhamis. 

Mutanen goma sha daya din da Hisbah ta kama, maza uku ne sai kuma mata takwas, inda ta cafke su suna cin abinci da rana a jihar a daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da azumi. 

Dr. Aliyu Musa Kibiya, Babban Darakta a hukumar ta Hisbah ya shaida cewa suna gudanar da bincike kan wadanda ta kama da kuma sanin dalilan da ya sanya ba sa azumi kamar yadda ya tabbatar wa da BBC. 

A cewarsa, sun kama mutane ne a yankuna daban-daban na jihar, yana mai cewa rashin yin azumin abin takaici ne.

"Mun kamo mutum 11 - mata takwas, maza uku wadanda aka same su a cikin wannan yanayi. Za mu tantance wala'alla wani yana da wani uzurin da idan mun kalla mun ga karbabben uzuri ne shikenan; wanda kuma aka ga haka nan ya yi irin wannan dabi'ar sai a bi matakai wajen yi masa nasihohi da kuma duk abin da ya kamata na bin doka da hukunta shi," in ji Dr. Kibiya.

Babban daraktan na Hisba ya ce bai kamata a ga "mace a bainar jama'a kin zo kina cin abinci ba, komai uzurinki."

Ya kara da cewa hukumarsa za ta ci gaba da kama duk wanda ta gani yana cin abinci a lokacin Azumi.

"Duk masu irin wannan halayyar a cikin mutane, ba sa kunyar Allah ba sa kunyar mutane, lallai za mu ci gaba da bibiyarsu ana daukar matakin da ya dace," a cewar Dr. Kibiya.

Wasu mazauna jihar ta Kano suna goyon bayan irin wannan mataki yayin da wasu ke ganin hakan bai kamata ba kasancewa Musulunci ya bai wa wasu rukunai na mutane damar sauke Azumi, kana bai tilasta musu cin abinci a boye ba.

A kowacce shekarar hukumar ta Hizbah na gudanar da irin wannan kame a cikin birni da kanana hukumomin Kano.

Azumi dai wajibi ne kan duk wani musulmi baligi mai cikakken lafiya a watan Ramadan, sai dai idan akwai dalili mai ƙarfi ko uzuri ga mata masu haila ko tsoffi da ba sa jure yunwa.

No comments