Hukumar 'Yan Sanda Ta Yi Sabon Mukaddashin Shugaba Bayan Buhari Ya Tsige Adamu


Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Usman Alkali Baba (DIG) a matsayin mukaddashin Sufeton Janar na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Hakan na nufin zai maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu wanda Buhari ya nada a ranar 15 ga watan Janairun 2019.

Ministan hukumar kula da sha’anin ‘yan sandan kasar Maigari Dingyadi ne ya fadawa manema labarai wannan sauyi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Mai baiwa shugaba Buhari shawara kan al'amuran kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmed, ya ruwaito Dingyadi yana cewa, "sabon nadin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba."


Shekarun yin ritayar Adamu sun cika tun a farkon shekarar nan, amma duk da haka Buhari ya kara mai wa'adin watanni uku, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce. Sai dai kafin kammalar wa'adin wata ukun, shugaba Buharin ya tsige shi. 

Post a Comment

0 Comments