Ina Gama Mulkin Kaduna A 2023, Zan Bar Jihar, Inji El-Rufai


Daga Muhammad Farouk

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada tabbacin cewa da zaran ya kammala wa’adin mulkinsa a 2023 zai bar jihar baki daya.

Gwamna El-Rufai ya ce saboda ma rashin son zamansa a jihar ne ya sanya gidansa na Unguwar Sarki kawai ya mallaka duk fadin jihar.

El-Rufai ya jaddada manufarsa na sake rage yawan ma’aikata a jihar musamman wadanda ba su cancanta ba a cewarsa da kuma wasu da ya bai wa mukaman siyasa. 


El-Rufai, wanda ya shekara biyu yana wa’adinsa na biyu, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta kafafen yada labarai ta gidajen rediyo na jihar. 

Gwamnan ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta rage ma’aikata daga cikin tsarin biyan albashi na jihar. 

“Bana satar kudaden gwamnati, bawai muna satar kudaden gwamnati bane don gina gidaje. Ina da gida ne a Unguwar Sarki kuma har zuwa yau shi ne gida daya tilo da na mallaka a Kaduna saboda bayan mulki na, ba zan zauna a Kaduna ba. Don haka, ba zan kara wani gida a jihar ba,” inji shi.

“Gwamnatin jihar ba za ta biya albashin mutanen da ba sa aiki ba, saboda haka, lamarin zai shafi ma’aikatan da ba su cancanta ba da wadanda ke sama da shekaru 50 ciki har da wadanda ma ba sa zuwa aiki a kai a kai kuma duk da haka ana biyansu albashi", inji shi. 

Game da wadanda aka nada a mukaman siyasa, ya ce, “muna duba yiwuwar rage nade-naden mukaman siyasa ne saboda idan ka rage wasu ka kasa rage naka, hakan zai zama rashin adalci. Tabbas za mu bincika mu rage wasu daga cikinmu a zahiri, tuni mun fara aiwatar da tsarin.”

Ya shawarci wadanda abin zai shafa da su je su nemi wani aikin, yana mai cewa an zabe shi ne don yi wa mutanen jihar aiki kuma zai yi iya bakin kokarinsa.

Post a Comment

0 Comments