Inyamurai Sun Fi Samun Aminci A Arewacin Nijeriya, Cewar Kungiyar Ibo Ta Ohanaeze

 


Babbar kungiyar 'Yan  kabilar Igbo dake Nijeriya ta bayyana cewar babu inda 'ya'yanta ke samun damar zaman lumana da kuma gudanar da harkokin su cikin kwanciyar hankali kamar yankin arewacin kasar.

Shugaban kungiyar a jihohi 19 dake arewacin Nijeriya Augustine Amaechi shi ne ya shaidawa wani taro a Abuja hakan, inda ya ce yankin arewacin kasar ya rungumi 'yan kabilar Igbo fiye da yadda ake zato wajen ba su damar gudanar da harkokinsu ba tare da tsangwama ba, abin da ya taimaka musu wajen samun ci gaba.

Amaechi wanda ya ce akan dan samu matsala nan da can amma wannan ba wani abin da zai tada hankali bane musamman a kasar da take kokarin ci gaba.

Dangane da batun kafa kasar Biyafara kuwa da wasu 'Yan kabilar Igbo ke fafutuka a kai, shugaban  kungiyar ya ce matsalar rashin ayyukan yi a yankin ya sa wasu daukar wannan matsayi, inda ya kara da cewa a matsayin su na 'Yan kabilar Igbo na 'yan kasuwa suna matukar bukatar yankin arewa domin habakar sana'oin su.

Amaechi ya ce duk da fushin da matasa suke da shi da kuma bukatar ballewa daga Nijeriya, su bukatar su ita ce sake fasalin kasar amma ba raba ta ba, domin babu hanyar da za a sarrafa kaya a kauyen ku kuma ka yi kasuwa kamar yadda ake yi yanzu a kasuwar Alaba dake Legas.

A na shi jawabi Shugaban kungiyar Ohanaeze na kasa George Obiozor ya bayyana cewar 'yan kabilar Igbo ba sa yaki da kowa, sai dai suna bukatar ganin an ba su hakkin su na 'yan kasa, kuma suna bukatar zaman lafiya da hadin kai da kowanne bangare.


Post a Comment

0 Comments