Daga Muhammad Haruna
'Yan kungiyar IPOB sun kashe sojoji guda biyu a daidai inda
sojojin ke tsayawa a Timber Junction area dake karamar hukumar Afikpo North a
jihar Ebonyi.
Jaridar The Nation ta labarto cewa;
lamarin ya auku ne da misalin karfe tara na dare. “’yan bindigar sun yi awon
gaba da kwanson harsasai na sojoji biyun da suka kashe”, inji majiyarmu.
Majiyarmu daga inda lamarin ya auku
wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya labarta cewa; wadannan ‘yan bindigar sun
isa mashigar sojojin ne a farar mota kirar Bas, a daidai lokacin da kuma
sojojin suka tsare su a wurin domin bincikensu, kawai sai suka bude musu wuta.
A cewarsa, kashe sojojin ya haifar
da tsoro da firgici a garuruwan Amasiri da Afikpo, domin mazauna garuruwan
cikin tsoro da firgici musamman masu sayar da kayayyaki a wurin suka kwashe
kayansu suka gudu gida.
“lallai abin takaici ne da tashin hankali a
wurin. An ce wadansu ne da ake zargin ‘yan bindiga ne wanda suka zo mashigar
sojojin ta Timber Shade da ta hada garuruwan Ehugbo da Amasiri a farar mota
kirar bas”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa; “kamar yadda aka
saba, sojojin suka tsayar da su domin bincike, tsayar da su ke da wuya suka
budewa sojojin wuta, biyu daga cikin sojojin mace da na namiji suka rasu,
sauran suka gudu”, ya tabbatar.
“wurin shiru yanzu kamar makabarta. Wurin
yana da yawan cunkoson jama’a, amma yanzu ba kowa. Mafi yawan al’ummar kauyakun
manoma da ‘yan kasuwa ne”, ya jaddada.
Ya kuma tabbatar da cewa; sakamakon
abin da ya faru mutane da dama sun gudu gida. “a yanzu da nake magana da kai,
ko’ina a kulle. Ko’ina shiru. Akwai tsoro a tsakanin mutane, dan uwana ina gaya
maka duniya ta kawo karshe kawai”, ya bayyana cikin tsoro.
Ya zuwa hada rahoton nan, rundunar
sojin Nijeriya ba su ce uffan ba a kai.
0 Comments