Mawallafin jaridar Daily Nigeria a Intanet Jaafar Jaafar ya shiga ɓuya bayan fuskantar barazanar tsaro a cikin kwanakin nan. Wasu maji...
Mawallafin jaridar Daily Nigeria a Intanet Jaafar Jaafar ya shiga ɓuya bayan fuskantar barazanar tsaro a cikin kwanakin nan.
Wasu majiyoyi na kusa da shi sun ce “rayuwar Jaafar Jaafar na cikin hatsari saboda wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suna farautarsa a gidajensa da ke Abuja da Kano."
Ana ganin wannan bai rasa nasaba da labarin da ya buga na sakin hotuna sama da goma sha biyar a 2018 da ke nuna yadda gwamnan Kano ke karbar na goro daga hannu 'yan kwangila.
Gwamnatin Kano ta sha alwashin ɗaukar mataki kan hutunan bidiyon inda ko a hirar da ya yi da BBC a watan Maris, Gwamnan Kano ya nanata cewa za su ɗauki mataki kan wanda ya saki bidiyon.
Wasu rahotanni sun ce Ofishin babban Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya ta gayyaci Jaafar Jaafar domin amsa tambayoyi kan zargin rura wutar rikici da kuma yaɗa labaran ƙarya ga babban Sufeto Janar na ƴan sanda.
No comments