Jami'an Tsaron Jami'ar ABU Sun Afkawa Mabiya Darika Masu Wazifa

Daga Wakilinmu

A cikin daren Alhamis ne Jami'an tsaron hukumar Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a karkashin jagorancin Malam Ashiru T Zango suka dirarwa dalibai masu wazifa a wani masallaci dake cikin harabar Jami'ar majiyarmu ta tabbatarwa da Jaridar MADOGARA

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin mabiya Darikar Tijjaniyya dake harabar Jami'ar don sanin abin da yake faruwa. Farfesa Gwadabe na daya daga cikin Uba a cikin mabiya Darikar Tijjaniya a Jami'ar da kasa baki daya.

A bayaninsa ya tabbatar da batun kama dalibai masu yin wazifa a harabar masallaci, inda ya ce bayan dukan kawo wuka da Jami'an suka yi musu. Ya ce yanzu haka daliban suna tsare a hannun jami'an tsaro kuma lafinsu daya shi ne suna yin salatin Annabi (SAW) a cikin masallaci na minti 15 a yini daya.

Farfesan ya kara da cewa ya yi iya bincike don ya gano lafin yin salati a masallaci amma bai samu ba.

Wanda ya ce a don haka ne ma yake kira da bbban murya cewa wajibi ne shugaban Jami'ar ya san abin dake faruwa don daukar matakin gaggawa. 

Kuma ya kara da cewa shugaban sashen tsaro na Jami'ar tuni ake zarginsa da nuna akida a cikin aikinsa wanda hakan ya sabawa dokar aikin da aka bashi.

Farfesa Gwadabe ya ce a don haka wajibi ne Hukumar Jami'ar yasa baki don babu wanda zai ce mabiya Darikar Tijjaniya sun taba tayar da hankali a duk inda suke gudanar da addu'o'insu.

Ya kuma yaja hankalin hukuma akan irin shugabancin da shugaban riko na tsaron yake yi, wanda ya ce idan har ya ci gaba da nuna akida a cikin aikinsa, to zai jefa Jami'ar a cikin rudani.

Farfesa ya karkare da cewa za su bi maganar don ba za su zura idanu ba a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro don kamata ya yi a gudanar da bincike kafin daukar matakin duka da kamu don kowa nada damar gudanar da addininsa bisa fahimtarsa.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban sashen tsaro na Jami'ar Malam Ashiru  T Zango amma bai daga wayar ba har zuwa hada wannan rahoton. 

Ya zuwa hada wannan labarin dalibai da Malamai mabiya Darikar ta Tijjaniyar na ta tofin Allah ya tsine ga matakin shugaban sashen tsaron.

A gefe guda kuma mabiya kungiyoyin da ba sa ra'ayin Darikar Tijjaniyya din na kara damara akan marawa shugaban tsaron baya.

Sai dai wakilinmu ya labarto mana cewa; amma komai na iya faruwa bisa la'akari da yadda jama'ar bangarorin biyu ke kara hassala cikin makaranta da wajenta.

Post a Comment

0 Comments