Jami’an Tsaron Nijeriya Sun Kashe Kwamandan IPOB

       Nnamdi Kanu, shugaban IPOB

Jami'an tsaron Nijeriya sun kashe wani babban kwamandan kungiyar IPOB a ranar Asabar kamar yadda BBC HAUSA ta labarto. 

Tawagar jami'an ta musamman ta hada da 'yan sanda da sojoji da kuma na DSS sun kai wani samame ne hedikwatar mayakan IPOB din da ke kauyen Awomama a Karamar Hukumar Oru ta gabas a jihar Imo da ke kudancin kasar.

Jaridar PRNigeria ta ce yan kungiyar IPOB din sune aka dorawa alhakin harin da aka kai hedikwatar 'yan sanda ta jihar da kuma gidan yari a ranar 5 ga watan Afrilun 2021.

Sun kara kai jerin wasu hare-hare kan jami'an tsaro a kudu maso kudu da kuma kudu maso gabashin kasar.

Wata majiya da ta shaida wa PRNigeria yadda lamarin ya faru ta ce an yi dauki ba dadi tsakanin yan IPOB din da kuma jami'an tsaron kafin su samu nasarar kashe kwamandan.

"A wani ba ta kashi da aka yi ta hadin gwiwa, an samu nasarar kashe kwamandan kungiyar IPOB a kudu maso gabashi wanda ake kira da Ikonso tare da wasu mutum shida.

"Sunan kwamandan Ikonso kuma shi ne mataimakin shugaba da ke tsara hare-hare da kungiyar take kai wa. Shi ne ya kitsa yadda aka kai hari kan hedikwatar 'yan sanda ta Imo da sauran hare-haren da aka kai wa jami'an tsaro a jihar."

Yayin musayar wutar an ji wa 'yan sanda uku da wani soja daya rauni, wadanda a yanzu haka suna can ana musu magani.

Post a Comment

0 Comments