Jami'ar MAAUN Ta Taya Sabon Shugaban Kasar Nijer Bazoum Murna


Hukumomin Jami'ar Maryam Abacha American University dake Nijer (MAAUN) a Maradi, ta taya sabon shugaban kasar Jamhuriyyar kasar Nijer, Muhammad Bazoum murnar kaddamar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Nijer din. 

Bukin kaddamar Mohamed Bazoum a matsayin shugaban kasar, ya gudana ne a ranar Juma'ar 2 ga watan Afrilun 2021 a filin taron na kasa da kasa na Mahatma Gandhi dake birnin Niamey. 

Shugaban rukunonin Jami'ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo shi ne ya bayyana sakon taya murnar ne a madadin Jami'ar a sakon  ya aika na taya murna ga sabon shugaban Nijer din wanda kuma ya sanya hannu, wanda ya rabawa manema labarai a Kano a ranar Juma'a. 

Da yake taya sabon shugaban murnar shiga ofishinsa, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi addu'ar Allah ya taimaki sabon shugaban ya kuma ba shi basira da ikon gudanar da shugabancin kasar. 

Jami'ar 'Maryam Abacha American University' ta bayyana Mohamed Bazoum a matsayin jajirtaccen shugaba wanda zai kawo wa kasar ci gaba a bangarori daban-daban. 

"Muna addu'ar yadda ya shiga ofishinsa, muna rokon Allah yasa ya yi nasara". 

Hukumar Jami'ar ta bayyana fatan ta na karfafa  kyakkyawan alakar dake tsakanin Jami'ar da tsohuwar gwamnatin Mahamadou  issoufou, inda ta ce tana fatan sabuwar gwamnatin Mohamed Bazoum da Jami'ar za su ci gaba da wannan. 
 
"Hukumar gudanar da Jami'ar na yi wa tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou fatan alheri da samun nasara da taimakon Allah a dukkanin lamuransa". 

Post a Comment

0 Comments