Jami'in Sojan Ruwa Ya Yi Ta Maza Ya Kwato Daga Hannun 'Yan BindigaTsohon Kakakin rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar Usman Kukasheka (mai ritaya), ya wallafa wani labari a shafinsa na Facebook da ke nuni da yadda wani jami'in sojon ruwan Nijeriya wanda aka yi garkuwa da shi tun ranar 24 ga watan Fabarairun 2021 a hanyarshi ta zuwa Kebbi bayan hutu da ya dauka. 

Sojan ruwan ya samu 'yancinsa ne bayan ya shafe kusan wata biyu a hannunsu. A zaman da ya yi a wurin 'yan bindigan ne ya karanci harkokinsu da yadda suke da gudanar da rayuwarsu, da kuma nakasansu, inda rana guda ya farmaki dan bindiga guda daya, ya kwace bindigarsa, inda ya kashe 'yan bindigar guda biyu nan take da bindigar da ya kwace. Wanda hakan ya ba shi damar tserewa. 

Post a Comment

0 Comments