Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Sanata Bello Hayatu GwarzoShugabancin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Gwarzo ya dakatar da tsohon mai tsawatarwa na majalisar Dattawa, Sanata Bello Hayatu gwarzo daga jam’iyyar bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa a yayin zaben shekarar 2019.

A wata takardar dakatarwa mai dauke da sa hannun shugaba da Sakataren jam’iyyar na mazabar Gwarzo, Idris Abdullahi Dan Baba, Jam’iyyar ta ce ta dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo na tsawon watanni 6.

Dakatarwar wacce ta fara aiki daga ranar 20 ga watan Afrilu a cewar jam’iyyar an yi ta bisa gazawar Sanata Bello Hayatu Gwarzo na gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Idan za a iya tunawa dai, rikicin jam’iyyar na PDP ya kara kamari ne biyo bayan abinda ya faru yayin zaben shugabancin jam’iyyar na Arewa maso yamma a jihar Kaduna.

Post a Comment

0 Comments